Posts

Showing posts with the label War

Yaƙin Isra'ila da Gaza Son Kai ne Ƙarara na Netanyahu

Image
Firaministan Isra'ila Binyamin Netanyahu Tunda rikicin Isra'ila da Yankin Zirin Gaza ya ɓarke a Gabas ta Tsakiya, ranar bakwai ga watan Oktoba na shekarar nan, duniya ta yi Allah wadai da salon yaƙin da kuma muhimmin goyon baya kamar su tallafin kuɗi, makaman yaƙi, da bayanan sirri da ƙasar Amurka ke ba wa ƙasar Isra'ila. Wannan yaƙi ba ƙaramin sarƙaƙiya ba ne dashi domin a yanzu haka, ƙasar Amurka tana ta ƙoƙarin haɗa kan ƙasashe da ƙungiyoyi masu faɗa aji a wannan yanki don kawo ƙarshen rikicin. Sai dai babban ƙalubale da ake fuskanta yanzu shi ne, Firaminista Bibi Netanyahu ya nuna aniyar dulmiyar da yankin gaba ɗaya cikin mummunan rikici.  Netanyahu ya fahimci cewa rashin wannan rikici zai zama babban kalubale ga makomar siyasar sa a ƙasar. Da zarar an ce yaƙi ya ƙare, za a gudanar da zaɓe a ƙasar Isra'ila, wanda zai iya haifar da rasa kujerarsa ta Firaminista. Amma idan yaƙin ya ci gaba, zai ci gaba da riƙe madafan ikon ƙasar, domin cika burinsa na zama...