Ɗan Adam Butulu Mai Saurin Mantuwa

Har yanzu na kasa fahimtar dalilin yaron nan 

Na daɗe ina jin mutane suna cewa ɗan Adam butulu ne amma ban taɓa tsammanin haka butulci yake ba. Ban taɓa tsammanin butulci yana da raɗaɗi idan aka yiwa mutum ba sai yau. Koda yake nasan cewa a wannan zamanin alheri yakan zama sharri a lokuta da dama. Amma ban taɓa tunanin sharrin yakai girman abinda nagani yau ba. Yau naga abin takaici har sai da nayi nadama, nayi kukan zuci.

Amma kafin na faɗa muku wanda yayi wannan mummunan butulci, bari nafara faɗa muku ginshiƙin labarin. Shekaru kamar uku zuwa huɗu da suka wuce, akwai wani yaro mai suna Gambo yana zuwa gidan mu da safe yana ɗan wanke-wanke da shara ana bashi abinci wani lokaci ma har da na saka kati a waya ake bashi. Domin duk dan a kyautata masa.

Ya kwana biyu yana aiki a gidan mu har aka gano idan ya gama aikinsa na safe yawon sharholiya na banza yake tafiya. Babu makarantar Arabic ballantana ta boko. Wannan aiki shi kaɗai yake yi domin yasamu yaci abinci. Bayan an gano haka, shikenan wata rana da yazo sai aka tambaye sa shin yana zuwa makaranta ko ba ya zuwa? Buɗewar ba kin ke da wuya sai yace, “bana zuwa makaranta.”  Ya ƙara da cewa shi iyayensa “basu da ƙarfin da zasu saka shi yayi karatu.” Allah Sarki.

Shikenan sai a gida aka ce to tunda abin haka ne, za'a saka shi a makaranta domin ya daina yawace-yawace na iska. Bugu da ƙari, aka kuma ƙara ɗauke masa nauyin abincin rana da na dare a maimakon na safe kaɗai da yake karɓa. Shikenan aka je aka kai shi makaranta a unguwar su kusa da gida aka sakashi a boko da safe, islamiyya da yamma. Da safe idan yazo yayi aikinsa sai yaci abinci ya wuce makaranta; da yamma kuma sai ya garzaya islamiyya.

Da farko-farko, kullum yana zuwa na makaranta baya fashi. Daga bisani wuyan sa yayi ƙwari sai ya fara laɓewa idan ya tafi — ma'ana ya daina zuwa kullum. Amma duk a gida babu wanda yasan yana yin hakan. Bugu da ƙari, har takai idan ya karɓi kudin biya na makaranta sai yaƙi kaiwa yaje ya kashe abunsa. Har takai ta kawo malamai suka fara korosa daga makaranta saboda ya jera lokuta da dama baya biyan kuɗin makaranta. Shikenan aka samu labari a gida akan abubuwan dake faruwa tattare da shi. Sai aka haɗani dashi muka je makarantar na kiyo kan zancen. Sai na dawo aka bani na kai kuɗaɗen da ake binsa. Malaman sa suka ce to za'a mai bulala saboda satittikan daya ɗiba baya zuwa. Nan take nayi na bada baki akan dan Allah suyi haƙuri kar su more shi. Dalili kuwa shine hakan zai iya hanasa dawowa gobe. Tun daga lokacin nan nine nake kai kuɗin sa na makaranta, idan kuma aka turo gida akan baya zuwa nine nake sakashi a gaba na mayar dashi. Duk wai dan karya zama babu karatun boko ko na Mahammadiya.

Yanzu yaron ya ɗan girma kuma yakai kimanin shekaru biyu baya aiki a gidan mu. Yafara tuka mashin mai ƙafa uku wato keke-napep. To mudawo kan batun butulci dana fara kokawa a farkon labarin nan. Ɗazu da misalin ƙarfe biyu da ƴan mintuna an aike ni wata unguwa. Sai na fito bakin hanya ina jiran mai keke-napep. Sai kwatsam na tsayar da mashin, ɗaga kan da zanyi sai naga yaron nan Gambo shine direban mashin ɗin dana tsayar. Dama mu biyu muka fita da wani yaya na amma kowa guri daban ya nufa. Aikuwa sai nace masa, “la wannan kamar Gambo, kaga har ya ajiye gemu amma ni ko ziri ɗaya bani dashi.” Akayi dariya na hau mashin ana ta raha ana tuna baya. Sai muka fara zuwa muka sauƙe yayana dama shima gurin da zashi kan hanya ɗaya yake da inda zani. Bayan ya sauƙa sai nafaɗawa Gambo ga unguwar da zai kaini. Kawai sai naga ya tsaya cak da mashin, ya dube ni yace mun wai kuɗi na yafi ɗari biyu zuwa da dawowa. Karku manta yayana ya biya nashi. Bama wannan bane abin takaici, yaron nan saboda bashi da kirki cewa yayi shi bama wannan hanyar zai yi ba. Bayan duk rahar da mukayi, abin sai ya ɗaure mun kai. Saboda duk wani mutum da yake cikin Nguru yasan daga bakin junction na GRA zuwa Tsohuwar Tashar Machina Naira ɗari ne zuwa haka kuma dawowa.

Da naji abin wani banbaraƙwai, sai nace masa to sauƙe ni ka ɗauki iya kuɗin ka kabani canji. Aikuwa yaron nan idanunsa babu kunya ya ɗauki Naira ɗari yabani canjin ɗari ɗaya dama ɗari biyu na bashi. Saboda ɗan iska ne wai sai yace, “bari na mayar ka gida mana.” Saura kaɗan nace “ubanka ya goya kura ba wando.” Sai na cinye zagin. Amma duk da haka kafin yabani canjin nace mai yanzu Gambo misali ko kyauta nace ka kaini unguwar nan baza ka kaini ba? Na ƙara tuna mai nine Adamun nan da da yake zuwa ya kai kuɗin makarantar ka sannan kuma idan ka kwana biyu baka je ba yaje ya bawa malaman ku haƙuri kar su jibge ka. Banyi niyyar faɗin haka ba nasan saboda Allah akayi masa. Bai ce komai ba kawai sai yayi murmushi. Yayi wuf ya shige cikin mashin ɗin sa ya zuga gaba da gudu. Nima nan take na tsayar da wani mashin na ɗane aka dawo dani gida zuciya ta tana tafarfasa. Na jima ban samu ɓacin rai irin na yau ɗin ba wallahi.

Billahillazi wannan abin har yanzu yana bani takaici. Na kasa fahimtar dalilin da yasa yaron nan yamin haka. Ban roƙeshi ya kaini kyauta ko kuma yayi mun ragi. Amma tsabular ɗan tasha ne wai ni yayiwa wannan cin karen. Yau na sake fahimtar cewa lallai ɗan Adam mai saurin mantuwa. Kuma na ƙara fahimtar cewa taimako a wannan zamanin kawai sai dai mutum yayi shi saboda Allah badan mutum ya isa ba, ko kuma ya cancanci hakan ba. Saboda wanda kaga ya cancanci ka taimake shi to fa shine wanda zai munana maka anan gaba. Yau naga babu sani ba sabo. Allah ya shiga tsakaninmu da wanda zasu ci mana mutunci a rayuwar duniya.

Comments

Popular posts from this blog

Exploring the Health Benefits of Fura and Nono

How My First True Love Story Ended

An Overview of My NYSC Experience: What You Should Know