Shin Najeriya Zata Ƙara Samun Nagartaccen Shugaban Ƙasa irin Olusegun Obasanjo

Tun bayan dawowa tsarin demokraɗiyya a shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da tara (1999) babu wani shugaba daya kai matakin da Chief Olusegun Obasanjo yakai ƙasar nan a shekaru takwas da yayi yana mulkin farar hula. Duk da cewa Najeriya tafi samun kuɗaɗen shiga masu yawa a wannan lokaci.


Bayan wasu karance-karance dana yi cikin ƴan kwanakin nan akan Najeriya, na fahimci cewa Najeriya har yau ta kasa samun shugaba kamar Chief Olusegun Obasanjo. Ingantattun bayanai da fashin baƙi da manazarta tarihi da kuma tattalin arzikin ƙasa sukayi yanuna cewa Obasanjo yayi ƙoƙarin inganta rayuwar al'ummar Najeriya. Ya kawo tsarukan aiki masu nagarta wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa da kuma cigaban al'umma.


Ni baƙin cikina yau shine, mai yasa majalisar dokokin Najeriya da masu faɗa aji na cikin ƙasar suka dakatar da ƙudirin Obasanjo na yiwa dokar ƙasa garambawul da zata bashi damar komawa kujerar mulki a karo na uku. Wataƙila da yanzu mun wuce wannan babin daya addabe mu duba da kyan yawancin tsarin tafiyar da harkokin Najeriya.


Nasan zaku iya tunanin cewa bawa Obasanjo damar komawa karagar mulki a karo na uku babban kuskure ne. Amma ina so ku sani cewa sai anyi kuskure yawanci ake gane wasu bayanan alƙaluma. Ko a karan kanka kasan kuskure yakan kawo maka cigaba idan har kayi aiki da hankali bayan tafka kuskuren. Amma saboda son kai irin na shuwagabanni da masu faɗa aji na wannan lokaci suka dakatar da ƙudirin gyara ƙasar izuwa hanya madaidaiciya. Yanzu gashi kowa yana ji a jika. Kowa yana kuka.


Daga ƙarshe, ina baku shawara akan yin zaɓe mai inganci a shekara mai gabatowa. Ina mai muku gargaɗin maimaita kuskuren da muka tayi a shekarun baya. Ku nutsu, ku tantance, sannan ku zaƙulo shuwagabannin masu nagarta domin ceto ƙasa da kuma ƴan ƙasa daga dilmiya cikin gagarumin tekun masifa. Domin zaɓe mai gabatowa shine zai nuna cewa Najeriya zata fita daga cikin wannan ƙangin daya hana kowa rawar gaban hantsi.

Comments

Popular posts from this blog

Exploring the Health Benefits of Fura and Nono

How My First True Love Story Ended

An Overview of My NYSC Experience: What You Should Know